Babban bankin Najeriya ya malalo $364 miliyan a kasuwar hada-hadar kudin kasashen ketare
Babban bankin Najeriya watau Central Bank of Nigeria (CBN) a turance ya bayyana sanarwar malala makudan kudaden kasar waje da suka kai dala miliyan 364 a kasuwar hada-hadar kudin kasahen ketare na tsakanin bankuna.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanrawa da Mista Isaac Okorafo wanda ke zaman jami'in hulda da jama'a na babban bankin na Najeriya ya fitar jiya talata a Abuja.

Legit.ng ta samu labari a cikin sanarwar cewa jami'in Okorafor ya kuma ce haka ma babban bankin ya sake malalo wasu karin dala milian 100 ga sauran masu hada hadar kudaden canjin.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan bayan nan ne dai babban bakin ya fitar da wani tsari inda suka malalo Dala miliyan 195 domin masu kananun masa'antu.
Asali: Legit.ng