Yadda ake amfani da shuwaka wajen magance ko wane irin zazzabi
Harkoki na kiwon lafiya sun bayyana yadda ake amfani da ganyen shuwaka wajen magance zazzabi
Binciken masana kiwon lafiya da binciken masana ta fannin ci da sha wato 'NUTRITIONIST' ya bayyana yadda ake amfani da ganyen shuwaka wajen magance zazzabi na; cizon sauro, lassa, ebola da tyfod.
Likitoci da masana magunguna sun bayyana shuwaka a matsayin magani daga cikin magugunan zazzabi kowane iri.
KU KARANTA: Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi
Ga yadda ake amfani da shuwaka da sanadin ta:
1. Abu na farko shine; ta bayyana cewa idan kana cin shuwaka koda sau biyu ne a sati, to ba za kayi zazzabi ko wane iri ba.
2. Idan kuma kana fama da zazzabi, to ko a wane mataki ya kaika zaka warware ba tareda shan magani ba. Saboda a cikinta akwai kowane nau'in sinadari me warkar da zazzabi
3. Shuwaka tana da amfanarwa akan duk matsalar da zata sa ka yi amfani da magunguna irin su, Amoxaciline, Ampiclox, Paracetamol, Clarithromacilin.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng