Maniyyatan jihar Taraba 1100 za su tafi kasa mai tsarki a ranar Alhamis

Maniyyatan jihar Taraba 1100 za su tafi kasa mai tsarki a ranar Alhamis

- Isiaku Darius ya nada Lamidon Gashaka Alhaji Zubairu Sambo a matsayin Amirul hajj

- Gwamanatin jihar Taraba ta dauki nauyin mahajjata 177

- An dauki mallaman da zasu jagoranci alhazai a kasa mai tsarki

Kimanin maniyyata 1100 daga jihar Taraba zasu tafi aikin hajji a kasan Saudiyya a ranar Alhamis, nji sakataren hukumar kula da alhazai na jihar Taraba Alhaji Umaru Leme

Leme ya fada ma yan jarida cewa gwamnatin jihar ta daukin nauyin maniyyata 177 sai kuma kananan hukumomin jihar suka dauki nauyin 37

Maniyyatan jihar Taraba 1100 za su tafi kasa mai tsarki a ranar Alhamis
Maniyyatan jihar Taraba 1100 za su tafi kasa mai tsarki a ranar Alhamis

A jawabin sa ya ce gwamnan jihar Isiaku Darius ya nada Lamidon Gashaka Alhaji Zubairu Sambo a matsayin Amirul hajj din alhazan jihar.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu nan: An tsige kakakin majalisan jihar Edo Okonoboh

Ya ce gwamnatin jihar ta ba wa hukumar naira miliyan dari uku da goma N310m dan tabbatar da ingantacen aikin hajji.

Leme yace angama shirye-shiryen wajen zama da abin da maniyyata za su ci a Makka da Madina kuma an dauki mallaman da za su jagoranci alhazai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko me mata ke bukata wajen maza?

Asali: Legit.ng

Online view pixel