Ministan Ilmi Adamu Adamu ya shiga uku
- Adamu Adamu ya saba rubutu game da yajin aikin ASUU
- Yanzu haka Malaman Jami'a sun shiga yajin aiki
- Akwai dai aiki wur-jan-jan a gaban Ministan
Yanzu haka Ministan Ilmi A. Adamu ya shiga tsaka mai wuya a game da yajin aikin da Malama Jamia'a su ka shiga.
Yanzu dai haka Kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin da sai inna-ta-gani kuma Malam Adamu Adamu ne Ministan ilmi na kasar. Kowa dai yanzu ya zura idanu ya ga yadda za a kare. Wani Malamin Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya Kabiru D. Lawanti dai yace 'Yan siyasa duk saya su ke.
KU KARANTA: Gwamnati ta gargadi Yan Neja-Delta
A lokacin da Ministan Ilmi na yanzu Mallam Adamu Adamu yana rubutu a jarida ya saba sukar Gwamnati a duk lokacin da Malaman Jamia'a su ka shiga yajin aiki irin haka.
Tun kwanaki kamar yadda mu ka samu labari da dama na Malaman Jami'a sun zabi a tafi yajin aikin da sai inna ta gani saboda rashin jituwa tsakanin su da Gwamnati. Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a wajen masu karatu a halin yanzu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Matasa su na fushi da kama masu garkuwa da jama'a
Asali: Legit.ng