Rashin mazan aure yayi kamari a Najeriya a halin yanzu
- Mazan aure su na matukar wahala a halin yanzu
- A Najeriya abin na nema ya zama tashin hankali
- Mugun buri ne dai ya kawo wannan a Kasar
Bincike ya nuna cewa mazan aure na nema su zama kayan gabas a Najeriya don kuwa ana fama da rashin su a yanzu.
Gidan Rediyon Faransa ne tayi wani nazari inda aka ga cewa sha'anin mazan aure na nema ya ta'azzara a Najeriya. Irin burin da ake cikawa yanzu musamman iyaye ne ke dai kawo wannan babbar matsalar a halin yanzu.
KU KARANTA: Marayu 56000 za su fara karatu a Borno
Iyaye kamar yadda hira da aka yi da Jama'a ya nuna na neman mai kudin gaske wanda ya mallaki abin Duniya. Ganin matan sun fi maza yawa ga kuma fama da talauci hakan ya sa aka ake fama da karancin mazan da za su iya aure a wannan hali.
Kwanan nan wata mata mai suna Pauline Chemanang ta buge da nakuda yayin da ake kokarin zabe a Kasar Kenya. Nan take wannan mata ta haifi diya mace a filin kada kuri'a a Yammacin Garin Pokot.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Matan PDP a wani taron siyasa
Asali: Legit.ng