Rasuwar wata uwar gida a jihar Zamfara ya tada tarnaki

Rasuwar wata uwar gida a jihar Zamfara ya tada tarnaki

- Jama'a mazauna unguwar Yan Dorayi da ke jihar Zamfara har yanzu suna cikin dimuwa da juyayin rashin wata matan aure yar shekara 25 mai suna Naja'atu wadda akayi wa kisan gilla a cikin gidan ta.

Maigidan marigayiya Naja'atu, Mallam Yakubu Maradun wanda malami a kwallejin ilimi na jihar Zanfara da ke Maru ya bada cigiyan ta kwanaki hudu da suke wuce kafin daga bisani aka gano gawar har ta fara rubewa a wani daki da ke gidan ta.

Rasuwar wata uwar gida a jihar Zamfara ya tada tarnaki
Rasuwar wata uwar gida a jihar Zamfara ya tada tarnaki

A cewar makwabtan Naja'atu, ta bar gida ne da izinin mijinta domin take banki ta karbo lambar BVN wadda zatayi amfani dashin wajen rajistan N-Power, amma tunda ta tafi bata dawo ba.

Ganin cewa yamma yayi bata dawo ba, mijinta ya bazama cikin gari nemanta har daga bisani ya kai cigiya gidan rediyo. An ci gaba da neman ta a duk inda ake tsamanin za'a ganta har ma da asibitoci da ofishin rundunar yan sanda amma ba'a ganta ba.

Bayan an gaji da nema, sai mutane suka fara cire rai har ma wasu nayi ma mijinta ta'aziya, ana cikin hakan ne sai wani daga cikin dangin mijin yace yana jin wari a cikin gidan, daga baya suka gano cewa warin yana fitowa daga wani daki da ke kulle.

Maigidan marigayiya Naja'atu yace mukulin dakin yana hannun ta hakan yasa mutane suka balle dakin kuma suka gano gawar marigayiyan da allamun an shake wuyanta.

DUBI WANNAN: Birnin Maiduguri ya sha fargaba saboda kawanyar sojoji a ofishin majalisar duniya

A halin yanzu rundunar yan sanda sun tsare Mallam Yakubu da kuma wani mutum domin gudanar da bincike.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan, DSP Shehu Muhammad ya tabbatar da faruwan lamarin sannan yayi kira da jama'a da su dena yada jita-jita akan lamarin tunda har yanzu ba'a kamalla bincike ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel