Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki nauyin karatun hazikin dalibin nan da ya yi zarra a Jarabawar WAEC da JAMB a Jihar
Gwamnatin Jihar Jigawa ta gayyaci hazikin dalibin nan Abdullahi Shitu wanda shine ya zamo zakara a cikin dalibai da suka rubuta jarabawar WAEC da JAMB a fadin jihar ta Jigawa.
Mataimakin gwamnan Jihar Jigawa, barista Ibrahim Hassan Hadejia, ne ya tattauna da dalibin. Daliban ya samu rakiyar mahaifinsa da kuma shugaban daliban karamar hukumar Mallammadori, kwamarad Hussaini Ubali wanda aka fi sani da Baros.
A baya shafin Rariya ta buga labarin wannan dalibi, Abdullahi Shitu a matsayin dalibi da yay i zarra cikin daliban jihar Jigawa wajen lahe jarabawar WAEC da JAMB, bayan ya samu maki 306 a jarabawar JAMB sannan ya ci A dukkan darusa 9 da ya rubuta a jarabawar WAEC.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ba zai yi murabus ba - Inji sanata Sani Yarima
Tun bayan buga wannan labarin, mutane da dama daga sassa daban daban na kasar ke tururuwa don tayin basa tallafi gurin ci gaba da karatunsa.
Kalli hotunan a kasa:
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng