Hukumar NCC ta takawa kamfanin GLO burki
- Globacom na da shirin bada goron Juma'a a
- Hukumar NCC ta takawa kamfanin GLO burki
- NCC tace dole GLO ta dakatar da wannan tsari
Hausawa kan ce rijiya ta kawo ruwa sai kuma guga ta hana. NCC ta hana GLO barin Jama’a su ci bagas kamar yadda aka sa rai.
Jiya labari ya zo mana cewa masu layin waya na Glo za su gwangwaje kyauta a Ranar Juma’a a Najeriya muddin sun sa katin waya. Sai dai Hukumar NCC ts kasa ta takawa kamfanin na GLO burki yanzu.
KU KARANTA: Abubuwa sun gyara gyaruwa a Najeriya
Hukumar NCC mai kula da kamfunan sadarwa na kasar ta kira GLO ta janye wannan garabasa ba da wata-wata ba. NCC tace wannan ya sabawa yarjejeniyar da aka yi da kamfanin a baya.NCC ta ma nemi ayi mata bayani.
Jaridar The Cable tace babban Jami’in Hukumar Sunday Dare ya rubuta takarda ga kamfanin na GLO ya nemi ta tsaida wannan tsari da aa shirya sannan kuma aka gayyaci Shugaban kamfanin na Najeriya ya hallara a ofishin nan NCC da gaggawa.
A da masu layin za su hau yanar gizo a kyauta yau. Sai dai Hukumar NCC ta takawa kamfanin GLO burki. Ana kokari a dakatar da wannan bagas da GLO za ta bada.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Babu maganar a dauke wuta a Kasuwar Aba
Asali: Legit.ng