Bincike ya bayyana yawun baki na saurin warkar da rauni a jikin dan Adam

Bincike ya bayyana yawun baki na saurin warkar da rauni a jikin dan Adam

To dai daman hausawa sun ce ilimi kogi ne don wani binciken masana nazarin halittu ya bayyana cewa yawun bakin dan Adam ya na taimakawa wajen saurin warkar da rauni

Wani sabon bincike ya bayyana cewa yawun bakin dan Adam ya na kunshe da sunadarai wanda ke habaka saurin samuwar tashoshin jini wanda su ke taimakawa wajen warkar da rauni

A cewar wannan bincike da aka buga a kafofin sadarwa na yanar gizo na wata jaridar kungiyar bincike a kan nazarin halittu, (Federation of American Societies for Experimental Biology, FASEB) ya nuna cewa, akwai wani sunadarin 'histatin-1' da yake bunkasa tashoshin jini wanda su ke taimakawa wajen warkar da rauni cikin gaggawa.

Yadda yawun baki ya ke saurin warkar da rauni - Bincike
Yadda yawun baki ya ke saurin warkar da rauni - Bincike

Babban edita na jaridar, Thoru Pederson ya bayyana cewa, "sakamakon binciken ya bude kofofi da za a cigaba da dora bincike kuma da wannan yake tunatar da amfanin halittu da kuma kananan yara da su ke yawaitar tsotson raunukan su."

Wani farfesa akan nazarin kula da hakori na jami'ar kasar Chile ya ce, wannan bincike zai habaka sababbin hanyoyin don inganta hanyoyin kara yin zurfi a cikin nazarin halittu wajen tantancce banbance-banbance na fatu kala-kala wajen warkewar rauni.

KU KARANTA: An yankewa wata mata daurin shekara 16 saboda ta tsiyayawa saurayin ta soyayyen mai

Ma su wannan bincike sun yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen binciken na su kamar bincikar tashoshin jini na jikin dan Adam, kwanduwar kwai da yawun bakin dan Adam.

Ma su binciken su na yunkurin cigaba da wannan bincike wajen samar da hanyoyin habaka warkewar rauni a jikin dan Adam.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng