Kananan hukumomi 22 a jihar Borno basu zaunuwa sanadiyyar barnar da Boko Haram tayi
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa mayakan Boko Haram sun janyo ma al’ummar jihar dimbin asara na biliyoyin daloli, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
Babban sakataren ma’aikatar sake tsugunnar da yan gudun hijira da sabunta gine gine na jihar Borno, Yarima Saleh ne ya bayyana haka a ranar Talata 8 ga watan Agusta, inda yace sun asarar da aka yi ya kai na Naira triliyan 1.9.
KU KARANTA: Bunƙasa tattalin arziki: Jihar Kebbi zata fitar da Akuyoyi 2000 duk rana zuwa Saudiya
Saleh yace Boko Haram sun lalata gidaje 986, 453, azuzuwa 5, 335, asibiti 201, famfuna da rijiyoyi 1, 630, ofisoshin Yansanda da na gwamnati 800 da kuma tashoshin watsa wuta 726, wannan yasa kananan hukumomi 22 cikin 27 basu zaunuwa.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito babban sakataren yace zuwa yanzu sun kammala gyaran dukkanin gine ginen gwamanti da na jama’a a kananan hukumomi 14, inda gwamnatin jihar ta gine gidaje N25,000.
Wasu daga cikin gine ginen da aka yi sun hada da azuzuwan makaranta, asibitoci, ofishin yansanda, kasuwanni, tituna, fadar sarakai, kotuna, masallatai da coci coci, du kana gudanar da gine ginensu.
“Nan gaba kadan zamu fara aiki gagga gagga a kananan hukumomin Bama, Dikwa da Ngla, wasu ayyukan da muke yi suna garuruwan Mafa, Damboa, Chibok, Askira Uba, Mobar, Biu da Hawul.” Inji Yarima Saleh.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Kalli barnar da Boko Haram tayi:
Asali: Legit.ng