Kungiyar Real Madrid ta kara kafa tarihi a Duniya
- Kungiyar Real Madrid ta lashe Gasar UEFA Cup
- Real Madrid ta doke Manchester United da ci 2-1
- Dan wasa Isco da Caseimero su ka jefa kwallayen
Kungiyar Real Madrid ta lashe Gasar UEFA Cup na Zakarun Nahiyar Turai. Kungiyar Real Madrid ta doke Manchester United da ci 2-1a wasan.
Dan wasa Caseimero ne ya fara zura kwallo a wasan a minti na 24. Isco ne ya karawa Real Madrid kwallo ta biyu kafin a shiga sa'a guda na wasan. Sabon Dan wasan Man Utd Lukaku ne ya ci wa Kungiyar bayan golan Real Madrid yayi aman wata kwallo.
KU KARANTA: Buri na in samu 'ya 'ya 7 - Ronaldo
Kungiyar Real Madrid ta doke Manchester duk da babban Dan wasa Cristiano Ronaldo 'yan mintuna kadan ya buga a wasan. Real ta zama Kungiyar farko bayan AC Milan a shekarar 1990 da ta daga Kofin UEFA Super Cup sau biyu a jere.
Dama kun ji za a kara ne a kofin UEFA Super na Zakarun Turai tsakanin wadanda su ka lashe kofin Champions League da Europa League a kakar bara.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
.
Neymar ya bar Barcelona
Asali: Legit.ng