Wasan cin kofi: Man United za ta gwabza da Real Madrid

Wasan cin kofi: Man United za ta gwabza da Real Madrid

- Kungiyar Manchester United za ta gwabza da Real Madrid

- Za a kara ne a wasan cin kofin UEFA Super Cup a daren yau

- Dan wasa Cristiano Ronaldo zai hadu da tsohon Kulob din sa

A daren yau Manchester United za ta gwabza da Real Madrid a filin Philip II Arena da ke Skopje a Kasar Macedonia.

Wasan cin kofi: Man United za ta gwabza da Real Madrid
Manchester United za ta gwabza da Madrid

Za a kara ne a kofin UEFA Super na Zakarun Turai wadanda su ka kashe kofin Champions League da Europa League a kakar bara. A cikin kwanakin nan Real Madrid ta buga da Manchester United inda kamar sauran wasannin ta ta sha kashi.

KU KARANTA: Ronaldo na shirin barin Real Madrid

Wasan cin kofi: Man United za ta gwabza da Real Madrid
Real Madrid za ta goge raini da Manchester

Sai dai a yau Talata manyan 'Yan wasan Real Madrid din za su dawo. Babban Dan wasan Madrid kuma tsohon Dan wasan Man Utd Cristiano Ronaldo zai buga wasan. Haka kuma kyaftin din Real Madrid Sergio Ramos. Madrid ta lashe kafin a bara.

Ba shakka dai Kocin Manchester Jose Mourinho ya san irin illar da Real Madrid za ta iya amma dai shi ma ya kawo sababbin 'Yan wasa irin su Romelu Lukaku. Haduwar Kungiyar na karshe dai Real Madrid din Mourinho tayi nasara kan Koci Ferguson lokacin yana United.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dan wasa Neymar ya bar Barcelona

Asali: Legit.ng

Online view pixel