Yadda aka sassari Uba da Dansa a Kano bayan bindiga taki cinsu
Rahotanni sun kawo cewa a daren ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta, wasu ýan bindiga da baá san ko sun wanenen ba sun kai hari gidan wani mutumi mai suna, Alhaji Muhammadu Jali dake karamar hukumar Sumaila a jihar Kano.
A cewar shafin Arewablog.com, yan taáddan sun harbi mutumin tare da dansa amma harbi yaki shiga.
Hakan ne ya sa suka sauya akalar kai harin nasu, inda suka yi ta sara su.
A yanzu haka ai Uba da Dan nasa na kwance a asibitin garin Sumaila, suna jinya sakamakon mummunan rauni da ýan taáddan suka ji masu.
KU KARANTA KUMA: Rahoton Forbes na bana: Duba ko na nawa Dangote yazo cikin masu kudin duniya 10 bakaken fata
Ga hotunan a kasa:
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng