Mawakan Najeriya 3 da ke neman kujerar siyasa
- Mawakan Najeriya sun fara ganewa harkar siyasa
- Yanzu haka Samklef na neman kujerar Gwamnan Imo
- Mawaki Terry G kuma yana neman kujeru har biyu
Yanzu haka tafiyar da ake yi Mawakan Najeriya sun fara ganewa harkar siyasa don wasu sun fara tsunduma cikin harkar.
1. Samklef
Dr. Klef Noni wani mai shirya wakoki a Kasar ya fito takarar kujerar Gwamnan Jihar Imo a zaben da za ayi nan gaba.
2. Terry G
Fitaccen Mawakin nan Terry G shi ma ba a bar shi a baya ba. Terry G yana neman kujerar Gwamna ne da ma Mataimakin sa duk shi kadai a Jihar Benuwe.
KU KARANTA: Barayin Gwamnati na bukatar sirri
3. Yul Edochie
Haka shi kuma Dan wasan kwaikwayo Yul Edochie wanda 'da ne wurin shararren Dan wasan nan Peter Edochie ya fito takarar kujerar Gwamnan Jihar Anambra.
Haka kuma mun samu labari na musamman cewa wani Dan damben Duniya ya zargi matar sa da cin amanar sa da wani Dan dambe Danuwar sa ‘Dan Najeriya wanda kuma har ta kai ga rabuwar su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Gwamnoni sun kai wa Shugaba Buhari ziyara
Asali: Legit.ng