Kiwon lafiya: Amfanin man kwakwa guda 7

Kiwon lafiya: Amfanin man kwakwa guda 7

Binciken masana tattali da kiwon lafiya ya nuna cewa akwai sindarai a cikin kwakwa masu matukar inganta lafiyar jikin dan Adam a fanni daban-daban

Man kwakwa ya na da amfani wajen inganta lafiyar fata, gashi, rage nauyin jiki, taimakawa wajen tace abincin jikin mutum da bayar da kariya ga wasu cututtuka da mutum ka iya kamuwa da su.

Kiwon lafiya: Amfanin man kwakwa guda 7
Kiwon lafiya: Amfanin man kwakwa guda 7

1. Gyara fatar jiki

Ana amfani da man kwakwa wajen man shafawa a jiki wanda yana da matukar fa'ida ga ma su busashshiyar fata da waskane. Man kwakwa yana kara laushin fata da yadda yake warware tamushewa irin ta tsufa a jikin fata kuma yana fa'idantuwa ga ma su ciwon kyazbi.

2. Gyaran gashi

Man kwakwa yana bunkasa yalwar gashi kuma ya kawatar da shi wajen kyalli.Yana kuma bayar da kariya ta amosani da rashin karyewar gashi.

3. Ciwon Zuciya

Akwai sindarin lauric acid a cikin man kwakwa wanda ya ke taimakawa wajen rage tasirin hauhawar jini da da rage daskararren maiko wadanda daman su ne ma su assasa ciwon zuciya. Yana kuma fa'idantuwa wajen al'adar mata.

4. Rage nauyin jiki

Da yawan mutane su na kukan jikin su ya mu su nauyi saboda maiko da yawan teba a jikin su, man kwakwa wanda shima maiko ne amma ya na inganta narkewar duk wani daskararren maiko dake jikin mutum wajen assasasa lafiyar kayan cikin mutum.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta yi ram da wani dan kasar Sin da laifin zamba a jihar Kano

5. Kariya ga cututtuka

Man kwakwa yana bayar da garkuwa ga lafiyar jikin mutum sanadiyar sinadarai na lauric acid, capric acid da caprylic acid. Wadannan sinadai suna inganta kariya na kananan kwayoyin cututtuka irin su kuraje, cutar sanyi da cutar HIV mai karya garkuwar jikin dan Adam

6. Tace amfanin abinci

Akwai ma su fama da ciwon ciki wanda rashin saure tace abinci da su ka ci ke janyo musu, binciken masana kiwon lafiya ya bayyana ingancin man kwakwa wajen inganta wannan matsala ta rashin tace amfani abinci da wuri a cikin mutum.

7. Lafiyar Hakori

Akwai sinadarin calcium a cikin man kwakwa wanda yake inganta karfin hakori kuma yake bayar da kariya wajen cututtuka na hakori da kara mu su haske su zama farare tar.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng