Siyasar Kano: Jam’iyyar APC ta kwance ma gwamna Ganduje zani a kasuwa

Siyasar Kano: Jam’iyyar APC ta kwance ma gwamna Ganduje zani a kasuwa

Jam’iyyar APC ta kasa ta dauki wani mataki da ake ganin raba gardama ne akan cecekucen da ake fama da shi akan shugabancin jam’iyyar a jihar tsakanin tsagin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamna Abdullahi Ganduje.

Uwar jam’iyyar APC ta kasa ta gayyaci Umar Haruna Doguwa ne a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar zuwa taron da mukaddashin shugaban kasa yayi da shuwagabannin jam’iyyar su 36 na kasa.

KU KARANTA: Kishin ƙishin: PDP na shirin tsayar da Atiku takarar shugaban ƙasa, Fayose mataimaki

Jam’iyyar ta gayyaci Doguwa ne wanda ake ganin yana samun goyon bayan Sanata Kwankwaso, duk da ikirarin da shugaban APC tsagin Gwamna Ganduje, wato Abdullahi Abbas ke yin a cewa shi ne shugaban jam’iyyar na halaliya.

Siyasar Kano: Jam’iyyar APC ta kwance ma gwamna Ganduje zani a kasuwa
Haruna Doguwa daga dama

BBC Hausa ta ruwaito an tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyyar tare da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin taron da uwar jam’iyyar ta kira da Farfesa Yemi Osinbajo.

Cikin wata hira da yayi da majiyar Legit.ng, Umar Haruna Doguwa yace “Na halarci taron ne kamar yadda uwar jam’iyya ta saba gayyata tarukan jam’iyya a matsayin halastaccen shugaban APC na jihar Kano.”

Tun bayan darewarsa karagar mulki ne dai ruwa yayi tsami tsakanin gwamnan jihar Kaduna Abdullahi Ganduje da Sanata Rabiu Kwankwaso, hakan kuwa yayi tasiri wajen rarraba kan jam’iyyar APC a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Yan APC sun koka da jam'iyyar. kalla:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng