Kwalejin ilimi ta jihar Kano ta na neman taimakon shugabannin jihar

Kwalejin ilimi ta jihar Kano ta na neman taimakon shugabannin jihar

Kwalejin Ilimi ta jihar Kano ta na neman agaji na gwamna Ganduje da Sarki Sanusi na biyu wajen yin ruwa da tsaki a kan a maishe ta jami'ar ilimi

A jiya ne kwalejin ilimi ta jihar Kano (Federal College of Education, FCE Kano) ta ke rokon agaji na gwamnatin jihar da masarautar Kano wajen yin ruwa da tsaki a kan kara matsayin kwalejin zuwa jami'ar ilimi kamar yadda gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da yardar a watan Mayun 2015 daf da karshen shugabancin ta amma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce sam ba wannan magana.

Daliban Kwalejin ilimi ta jihar Kano su na neman taimakon shugabanni
Daliban Kwalejin ilimi ta jihar Kano su na neman taimakon shugabanni

Sabon ciyaman na kungiyar kula da harkokin kwalejin, Malam Salihu Lukman Abubakar ne ya nemi taimakon don gwamnatin Buhari ta yi duba zuwa ga al'amarin a yayin da kungiyar ta kaiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanasu na biyu ziyara.

A gidan gwamnatin ne, Lukman ya bayyanawa Ganduje cewa wani sanata daga cikin sanatoci ma su wakiltar jihar Kano ne ya mika wannan lamari ga majalisar a kan maishe da kwalejin ilimin zuwa jami'ar ilimi.

KU KARANTA: Yajin Aiki: Ma'aikatan kwalejin ilimi ta jihar Legas sun gyara zaman su

A bayanin Ganduje ya ce, kwalejin ta dade ta na bayar da gudunmawa wajen harkokin cigaban kasar nan kuma tun ba yanzu ba ta ke bayar da kwalin digiri.

Shi kuwa Sarkin Kano, ya bayyanawa kungiyar cewa abinda yake janyowa harkar ilimin kasar nan koma baya shine karancin kwararrun malamai a kasar nan.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel