Wata sabuwa! Jami'an Laliga sun ki amincewa da kudin cinikin Neymar
Labaran da ke iso mana yanzu suna nuni da cewa mahukuntan dake tafiyar da kasar nan ta kwallon Laliga a kasar Sifaniya ta ki amincewa ta karbi kudin cinikin dan wasa Neymar da suka kai dala miliyan 260.
A yau ne dai kungiyar PSG dake a kasar Faransa ta so biyan kwantaragin dan wasan daga kungiyar Barcelona domin ta dauke shi amma sai ba'a amshi kudin ba.
Legit.ng dai ta ruwaito a jiya cewa dan kwallon kafar na kungiyar Barcelona dake taka leda a kasar Spaniya ya nemi kungiyarda ta basshi dama don ya tafi zuwa kungiyar PSG dake can a kasar Faransa.
Daga bisani kuma sai itama kungiyar ta Barcelona ta tabbatar dahakan yayin da ce tabbas dan wasan ya rubuta mata takarda yana bukatar a barshi ya tafi yayin da kuma ya bukaci kungiyar ta PSG da ta saye kwantaragintasa da ta kai €222 miliyan.
Asali: Legit.ng