Wasu gawurtatun mafarauta 2 sun shiga hannun hukuma a Bauchi
- Hukuma ta cafke mutane 2 masu haramtaciyar farauta a garin Bauchi
- Mafarautan sunyi yunkurin kai hari ga jami'an hukumar gandun daji amma basuyi nasara ba
- Alkali ya yanke musu hukunci daidai da irin laifunka da suka aikata
Hukumar kulla da gandun dajin jihar Bauchi ta sama nasarar cafke wasu gawurtatun masu haramtaciyar farauta guda 2 masu suna Amos Bitrus da kuma Danjuma Sale.
An kama mafarautan ne a yankin Tungan-Baki da ke jihar Bauchi a ranar 30 ga watan Yulin wannan shekaran, an same su ga gwagwon biri guda 1, wasu birai guda 3, bauna guda daya, Aladun daji guda 2 da kuma zabuwa guda 1.
Mafarautan kuma suna tafe da karnukan farauta guda 7, kuma sunyi yunkurin fada ma jami'an gandun dajin da fada amma basu yi nasara ba.
DUBA WANNAN: Dalilin da yasa muka ki amincewa da Magu a matsayin shugaban EFCC - SarakiDalilin da yasa muka ki amincewa da Magu a matsayin shugaban EFCC - Saraki
Rahotanni sunce Alkali ya yanke ma Danjuma hukunci shekara biyu a gidan kaso, tunda a shekaran baya an taba samun sa da laifin farauta a gadun dajin Yankari. Shi ko Amos kotu ta yanke masa hukunci zama na wata 6 a gidan kaso tunda wannan ne laifin sa na farko.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng