Ka ji irin ribar da Dangote ya samu tun a tsakiyar shekara
- Kamfanin Simintin nan na Dangote ya samu riba a Afrika
- Dangote ya samu muguwar riba tun kafin shekara ba ta kare ba
- An samu karin ciniki na fiye da kashi 12 cikin 100 a Afrika
Kamfanin Simintin nan na Dangote wanda duk Nahiyar nan babu irin sa ya samu kazamar riba tun kafin shekarar ta kare.
An samu karin ciniki na fiye da kashi 12% na abin da aka saba samu a Afrika a farkon shekarar nan. Cinikin farkon shekarar nan zuwa karshen Watan Yuni sun nuna haka. Kamfanin simintin na Dangote dai ya tashi cak da kafafun sa a Duniya.
KU KARANTA: Aisha Buhari za ta kai ziyara Jihar Imo
A Najeriya kurum dai Kamfanin Dangote ya samu karin ciniki na kusan Naira Biliyan 300 ban da sauran kasashen da ke kusa irin su Zambiya, Habasha, Sanagal, Ghana, Kongo, Gambiya da sauran su.
Aliko Dangote yace a kowace rana ya kan yi aiki har na sa'a 18. Tun karfe 8:30 na safe Dangote yake shiga Ofis kuma ba zai fito ba sai bayan awa 18.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ko Miliyan 30 za ta canzawa mutum rayuwa
Asali: Legit.ng