Motoci nawa ake da su a kaf fadin Najeriya?

Motoci nawa ake da su a kaf fadin Najeriya?

- Ko ka san motoci nawa ne a faadin Najeriya

- Najeriya na shan kusan lita miliyan 40 na fetur

A yanzu haka akwai motoci kimanin Miliyan 11.5 a faadin Kasar nan. Mutanen Najeriya dai sun kai akalla mutane Miliyan 180. Hakan na nuna cewa a cikin mutum 15 akalla a samu mutu guda mai mota.

Motoci nawa ake da su a kaf fadin Najeriya?
Wurin saida motoci a Najeriya

Kashi 58.5% cikin motocin da ake da su a Najeriya na haya ne watau wadanda ake amfani da su wajen kasuwanci. Wadannan motoci ne su kafi kowane yawan hadari da kuma rasa ran Jama’a bisa titunan Najeriya.

KU KARANTA: An kashe Jamian kwastam a Katsina

Kashi 40.2% kuma na motocin da ake da su na jama'a ne watau na-kan su. Ana da motoci saa da Miliyan 4.5 wadanda su ke ba na hay aba. Akwai kuma wasu motocin na Jami'an Gwamnati da sauran Kungiyoyin kasa-da-kasa na kimanin kashi 1.4% wadanda wasu a kan mara masu baya.

NAIJ Hausa ta samu wannan alkaluma ne daga bakin Shugaban Hukumar tara alkaluman kasa watau Hukumar NBS Dr. Yemi Kale. Kwanaki kun ji cewa Alkaluman kasar sun tabbatar da cewa tattalin arzikin kasar ya kama hanyar mikewa sarai bayan ya durkushe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mota ta kashe wani dan siyasa a Legas

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng