Dandalin Kannywood: Jaruma Fati Muhammad ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa

Dandalin Kannywood: Jaruma Fati Muhammad ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan Fati Muhammad wadda ta fito a cikin tsohon fim din nan na Sangaya a matsayin Zubaina ba bayyana auren jarumi Sani Musa Mai Iska a matsayin babbar nadamar ta a rayuwa.

Jarumar ta bayyana hakan ne a cikin wata fira da tayi da jaridar Blue Print inda ta bayyana cewa ta amince da cewa kowa na da jarabawar da Allah ya ke yi masa sannan kuma tace ita dai jarabawar ta ta fannin aure take.

Dandalin Kannywood: Jaruma Fati Muhammad ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa
Dandalin Kannywood: Jaruma Fati Muhammad ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa

Legit.ng ta samu cewa a cikin firar da tayi da jaridar, jarumar ta kara nanata maganarta da tayi a baya inda tace ba fa zata kara auren dan fim ba koma waye.

Daga karshe kuma jarumar ta bayyana jarumi Ali Nuhu a matsayin wanda take darattawa fiye da kowa a masana'antar fim.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng