Karatu ne a gabana ba fim ko aure ba - Aisha Tsamiya
Fitaciyyar jarumar nan ta Kannywood Aisha Aliyu Tsamiya ta bayyana kudirinta wanda shine burinta a yanzu.
A wata hira da jarumar tayi da jaridar Premium Times ta bayyana cewa ita babban burinta a yanzu shine karatu ba wai harkar fim ko aure ba.
Jarumar t ace hakan ba yana nufin ta tsani aure bane kawai dai raáyinta ne domin karatu ne a gaban ta.
A cewar ta: “ Bawai ina nufin natsani aure ko bazan yi aure ba, a’a, ina nufin a yanzu karatun shine a gabana ba aure ko fim ba. Wannan shine yanayin yanda na tsara rayuwata.
“Amma kuma, bance dole sai hakan ta faru ba, Allah yanayin duk abinda yaso. Idan baiso ba ko karatun ba zanyi ba.
KU KARANTA KUMA: Daso ta nemi afuwar masaurautar Kano game da rike tagwayen MasuDaso ta nemi afuwar masaurautar Kano game da rike tagwayen Masu
“Ni dai kawai na fadi ra’ayinane, kuma kowa yana da yanda ya tsara rayuwarsa. Inji Aisha Tsamiya.”
Jarumar taci gaba da karatu ajami’ar A.B.U Zaria. domin yin digiri a fannin siyasa wato Political Science.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng