Daso ta nemi afuwar masaurautar Kano game da rike tagwayen Masu

Daso ta nemi afuwar masaurautar Kano game da rike tagwayen Masu

Fitacciyar jaruma ‘yar wasan Hausa mai suna Saratu Gidado da aka fi sani da Daso ta nemi yafiyarmasarautar Kano a bisa rike tagwayen masu da ta yi a cikin wani sabon fim da ake kan dauka a yanzu mai suna ‘Dan Tijara’.

Tagwayen masu dai ababe ne guda biyu masu launin kore da ja da sarakunan Kano ke amfani da su tun kafin zuwan Fulani, wanda ya samo asali tun zamanin wasu tagwaye sarakunan Kano da suka yi mulki a lokaci guda.

A cewar Daso bata taba tunanin cewa rike tagwayen masu zai zamo sabawa ga masarautar ba.

Ta bayyana cewa ta dauki hoto da masun ne sakamakon sha’awa da suke bata, kuma duba da cewa ba na ainihi ba ne, kamar yadda Nasir Zango ya rahoto a shafinsa na Facebook.

Daso ta nemi afuwar masaurautar Kano game da rike tagwayen Masu
Daso ta nemi afuwar masaurautar Kano game da rike tagwayen Masu Hoto: Alummata

A cikin fim din na ‘Dan Tijara’, jarumi Ali Nuhu ne ya fito a matsayin sarki inda ya yi ta sanya kayan sarauta na alfarma, har ma kuma ya rike tagwayen masun.

Yayin da ake daukan fim din ne wasu daga cikin jarumai mata kamar su Halima Atete, Mai Gado da ita Saratu Gidado suka yanke hukuncin daukan hoto da Tagwayen masun, lamarin da ya zame masu laifi.

KU KARANTA KUMA: An fara jigilar Maniyyata daga Najeriya zuwa kasa mai tsarki

Wata majiya daga fadar sarkin Kano ta ce rike wadanan masu ga wani sabawa dokar masarautar Kano ne domin anyita ne don sarki kadai.

Harma ta kara da cewa akwai wani zamani da wani sarki a masarautar Jigawa ya so mallakar masun ammamasarautar Kano ta taka masa birki.

Daso dai ta ce ta tuba a yafe mata da laifin da aka ce ta aikata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng