Yan Najeriya bakwai sun shiga cikin jerin attajiran Fastocin duniya guda 20

Yan Najeriya bakwai sun shiga cikin jerin attajiran Fastocin duniya guda 20

- Tsohon shugaban kungiyan CAN shine na bakwai a duniya

- Dan kasan Brazil shine na daya

- Dan takaran shugaban kasa a shekaran 2011 shine na ashirin

Jaridan Forbes ta saka jerin sunayen attajiran fastocin duniya na shekaran nan, kuma sunayen fastocin Najeriya guda bakwai ya shiga cikin jerin.Jaridan ta saka sunayensu tare da adadin kudaden da suka mallaka.

Jerin ya kunshi duka sunayen Attajiran Fastocin duniya wanda ya nuna shugaban cocin Kingdom of God dake Brazil, Pastor Edir Macedo shine na daya a duniya.

Sai kuma shugaban Living Faith Church, Bishop David Oyedepo shine na farko a Najeriya.

Yan Najeriya bakawai sun shiga cikin jerin attajiran Fastocin duniya guda 20
Yan Najeriya bakawai sun shiga cikin jerin attajiran Fastocin duniya guda 20

Ga jerin sunayen attajiran Fastocin duniya guda 20.

KU KARANTA:Duniya ina zaki damu: Jami'an yan sanda sun cafke yan luwadi 42 a wani otel din

1. Edir Macedo Fasto a kasan Brazil ya mallaki akalla $1.1b Shine mau cocin Universal Church of God. Macedo na daya a jerin masu kadi a Fastoci

2. Kenneth Copeland shine mai cocin Kenneth Copeland Ministreis. Ya mallaki $760m

3. Pat Robertson ya mallaki $500m. Pat Rpbertson shine shugaban cocin Southern Baptist Church

4. George Foreman kwararen tsohon dan dambe wanda ya mallaka $250m. Yanzu mai wa’azi ne a Church of lord Jesus Christ dake Houston. Kwanannan ya buga takarda mai taken “Allah na tare dani.

5. Bishop David Oyedepo Fasto ne dan kasan Najeriya. Shine shugaban cocin Living Faith Church world wide wanda aka fi sani da Winner Winners Chapel International World headquater. Oyedepo ya mallaki $150m shine na daya a jerin attajiran fastocin Najeriya da nahiyan Afrika.

6. Pastor E.A Adeboye shima dan Najeriya ne. Shine shugaban cocin Redeem Christian Church of God, ya mallaki $130m.

7. Bishop Ayodele Oritsejafor dan Najeriya ne kuma tsohon shugaban kungiyan CAN malaki $120m.

8.Uebert Angel shine shugaban Spirit Embassy Church ya mallaki $60m.

9. Pastor Chris Oyakhilome shima dan Najeriya ne kuma shine shugaban cocin Christ Embassy of Najeriya. Ya mallaki $50m.

10. Benny HInn ya mallaki $42m.

11.Joel Osteen shine shugaban cocin Lakewood Church Houston Texas. Ya mallaki $40m.

12. Fasto Tshifinwa Irene ya mallaki $ 32m

13.Creflo Dollar sananne Fasto ne Amurka ya mallaki $27m.

14. Fasto Ray Macaukay shugaban cocin Rhema Bible Church of God

15. Billy Graham ya mallaki $25m

16. Rick Warren shine shugaban Saddleback Lake Forest Carlifonia. Ya mallaki $25m

17. Bishop T.D. Jakes ya mallaki $18m

18.T.B.Joshua yana da cikin sanannun fastocin Najeriya shine shugaban cocin Synagogue Church of All Nations ya mallaki $15m.

18. Mathew Ashimolowo dan Najeriya ne kuma shine shugaban cocin Kingsway Interanational Christain Center dake Ingila. Ya mallaki $10m

19. Juanita Bynum dan kasan Amurka ne. ya mallaki $10m.

20. Chris Okotie dan Najeriya ne kuma shine shugaban cocin House of God. Ya mallaki $10m.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng