Duniya ina zaki damu: Jami'an yan sanda sun cafke yan luwadi 42 a wani otel din Najeria
1 - tsawon mintuna
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun bayar da sanarwar damke wasu kasurguman katti har su 42 a wani otal dake a jihar Legas suna luwadi.
Rundunar yan sandan ta jihar ita ce ta sanar da hakan ga manema labarai yayin da kuma tace ta yi hakan ne bayan da ta kai samame a otel din a dalilin wani kwarmato da ta samu.

Legit.ng dai ta san cewa neman jinsi daya a Najeriya haramun ne a dokar kasa sannan kuma abun kyama ne ainun a al'adu da kuma manyan addinan kasar.
A bisa mizanin doka kuma, auren jinsin ya haramta ne a cikin tsarin mulkin kasar tun bayan da tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya sanya wa dokar da take haramta hakan hannu lokacin da yana mulki.
Asali: Legit.ng