Gwamnati ko yan kasuwa? Har yanzu ana fama da matsalar tsadar kayan abinci - Rahoto
Wani bincike da aka gudanar ya nuna har yanzu fa kayayyakin masarufi suna nan da tsadar su duk kuwa da daminar da ake ciki da kuma yadda tuni anfanin gona ya fara nuna a wasu sassan kasar.
Binciken da kamfanin dillacin labarai na Najeriya watau News Agency of Nigeria (NAN) yayi ya bayyana cewa a garuruwa irin su Legas har yanzu buhunnan dankalin turawa, makani da ma masara duk ana saida su N8,000 ko ma fiye da hakan.
Legit.ng ta samu labarin cewa kuma daga binciken an gano cewa buhun wake kuma yanzu haka yana kai tsakanin N48,000 zuwa N49,000 yayin da kwano daya kuma na waken ya kai har sama da N1,000.
Abun tambaya anan shine shin me yasa kayayyakin masarufin ke da tsada sosai wai duk kuwa da daminar da muke a ciki. Shin laifin na yan kasuwa ne kukwa gwamnati.?
Asali: Legit.ng