Yanzu-Yanzu! An nada sabon sarkin Tsafe, kun san wanda aka ba?

Yanzu-Yanzu! An nada sabon sarkin Tsafe, kun san wanda aka ba?

Gwamnatin jihar Zamfara dake a arewa maso yammacin Najeriya ta nada Alhaji Muhammadu Bawa a matsayin samon sarkin Tsafe na 18 a tarihin masarautar tun bayan kafa ta.

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautun gargajiyar na jihar Alhaji Muttaka Rini shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai a Gusau babban birnin jihar.

Yanzu-Yanzu! An nada sabon sarkin Tsafe, kun san wanda aka ba?
Yanzu-Yanzu! An nada sabon sarkin Tsafe, kun san wanda aka ba?

Legit.ng dai ta samu labarin cewa hakan ya biyo bayan tsohon sarkin Alhaji Habibu Aliyu wanda ya rasu a asibitin koyarwa ta Usmanu Danfodiyo dake Sokoto a satin da ya gabata.

Kafin nadin sabon sarkin dain Alhaji Muhammadu Bawa shine shugaban ma'aikatar da ke kula da ayyikan gayya da kuma ci gaban jihar watau State Community and Social Development Projects (CSDP).

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng