Yaki: Kasar Koriya ta kara harba wani mugun makami mai linzami
- Kasar Koriya ta Arewa ta yi gaba wajen harkar nukiliya
- Kwanan nan Kasar ta kara harba wani makamin
- Wannan ne karo na biyu da kasar ta harba nukiliya
Mun samu labari cewa Kasar Koriya ta Arewa ta yi gaba wajen harkar nukiliya don kuwa Kwanan nan Kasar ta kara sakin wani mugun makamin.
Ku na sane cewa wannan ne karo na biyu da kasar ta harba nukiliya cikin 'yan kwanakin nan domin wani gwajin da ta ke yi. Makamin wannan karon ma dai ya fi wanda aka saki a baya. Kwanaki kasar ta saki irin wannan makami da zai iya barin Nahiya zuwa wata Nahiyar.
KU KARANTA: Nnamdi Kanu zai cika Legas da zugar sa
BBC ta rahoto cewa wannan makami ya dade yana yawo kafin ya fada cikin ruwa a wani Gari cikin Kasar Japan. Duk da dai takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke dorawa Kasar ta Koriya ta Kudu ba ta tsaya wajen harkar kera makamin ba.
Kwankin baya Kasar Koriya ta Arewa ta saki wani mugun makami mai linzami wanda ka iya dura kan Garin Alaska. Amurka tace dole a takawa Koriya burki ko ta karfi da yaji idan ta kama don ta saba doka bayan da ta saki wani mahaukacin makami mai linzami.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Tsohon Fursuna na nema a saki mutanen sa
Asali: Legit.ng