Labarai cikin Hotuna: Jama'a sunyi jinjina ga Buratai a masallacin Sarkin musulmi Bello da ke Kaduna
Dumbin masallata ne jiya a juma'a suka zagaye shugaban dakarun sojin kasa na Najeriya Laftanar Janar Tukur Buratai bayan ya kamalla sallar juma'a a masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwan Sarki a Kaduna domin jinjina masa.
Irin wannan nuna kauna da akayi masa bazai rasa nasaba da irin kokarin da yakeyi ba wajen yaki da ta'addanci a arewa maso gabashin Najeriya.
Hotunnan sun nuna Buratai sanye da jamfa da hula yana murmushi a yayinda da mutane ke masa jinjina ta ban girma.
KU DUBA: Abin tausayi: An kashe wani basarake an kone gawarsa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng