Dandalin Kannywood: An samu sabon jarumi mai kama da marigayi Ibro sak

Dandalin Kannywood: An samu sabon jarumi mai kama da marigayi Ibro sak

A yayin da masoya, yan uwa da kuma masu sha'awar kallon fina-finan Hausa ke ta jimami na rashin fitaccen jarumin nan na barkwanci watau Rabilu Musa IBRO, kwasam sai ga wani mai kama da shi ya bulla a masana'antar.

Matashin dai mai suna Alasan Kanu mazaunin Hotoro ne dake a jihar Kano a arewacin Najeriya ya fara fitowa fina-finai ne kwanannan inda kuma ya ke kwatanta barkwanci a ciki tamkar dai marigayin jarumin Rabilu Musa.

Dandalin Kannywood: An samu sabon jarumi mai kama da marigayi Ibro sak
Dandalin Kannywood: An samu sabon jarumi mai kama da marigayi Ibro sak

Legit.ng ta samu labarin cewa yanzu haka dai matashin sabon jarumin Alasan Kanu ya samu damar fitowa a wani sabon fim mai suna 'Jiki Magayi' wanda a ciki kuma ya taka muhimmiyar rawa.

Dandalin Kannywood: An samu sabon jarumi mai kama da marigayi Ibro sak

Idan ba'a manta ba dai Allah ya karbi ran marigayi Rabilu Musa Ibro ne kimanin fiye da shekara daya kenan bayan ya sha fama da gajeruwar rashin lafiya inda kuma har yanzu ba'samu wanda ya cike gibin sa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel