Ko ka san wanene Sulaiman Hassan; Sabon Minista a Gwamnatin Buhari
- A jiya ne Farfesa Yemi Osinbajo ya rantsar da wasu Ministoci
- Daga ciki akwai Alhaji Sulaiman Hassan daga Jihar Gombe
- Sulaiman ne ya maye gurbin Amina J. Mohammed daga Jihar
A jiya ne Mukaddashin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya rantsar da wasu Ministoci bayan an dauki dogon lokaci ba a maye guraben wadanda aka rasa ba. Daga ciki akwai Sulaiman Hassan daga Gombe. Ko wanene wannan?
1. Asalin sa
Sulaiman Hassan ya fito ne daga Jihar Gombe kuma ya maye gurbin Amina J. Mohammed wanda ta koma Majalisar Dinkin Duniya
2. Siyasa
Wannan mutumi ya dade tare da Shugaban kasa Buhari don ya rike Shugabancin tsohuwar Jam'iyyar su Buhari watau CPC a shekarar 2011 na Jihar Gombe.
KU KARANTA: An yi Shugaban kasa Buhari addu'a
3. Jakadan Najeriya
Ba a dade da Shugaba Buhari ya zabi Sulaiman Hassan a matsayin daya daga cikin wadanda za a tura Jakadancin kasar ba sai ga shi kuma an turo sunan sa a matsayin Minista.
4. Aiki
A bar ta siyasa, Sulaiman Hassan masani ne a harkar gine-gine. Hassan yana cikin Kungiyar Quantity Surveyors na Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ana kokarin ba matasa damar fitowa takara
Asali: Legit.ng