Dandalin Kannywood: Duk wadda ta ba da kanta don a sa ta fim laifin ta ne - Jaruma
Wata sabuwar fuska a cikin jarumai mata na masana'antar finafinan Hausa mai suna Khadija Abubakar Mahmood ta bayyana cewa duk macen da ta bada kanta don a sata a cikin fim laifin ta ne.
Jarumar tayi wannan kalami ne a cikin wata fira da tayi da mujallar nan ta 'fim' wadda take kowo labaran fina finan Hausa lokacin da take amsa tambayar da ake yi mata game da maidu'in.
Legit.ng ta samu labarin cewa dai jarumar ta kuma bayyana cewa ita babu wanda ya taba kusantar ta da irin wannan zancen yayin da kuma take fadan cewa wasu matan su ke bada kofar a yi masu hakan.
Haka ma dai jarumar a cikin firar ta bayyana wasu daga cikin fina finan da ta taba fitowa a cikin su da suka hada da Gidauniya, Sahun Baya, Uwar Miji da dai sauran su.
Asali: Legit.ng