Kotu ta daure wani mai sana'ar wanki da guga watanni 3 saboda ya saci tukunyar burkutu

Kotu ta daure wani mai sana'ar wanki da guga watanni 3 saboda ya saci tukunyar burkutu

Wata kotu mai mataki na 1 a kauyen Karmo dake a garin Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta yankewa wani matashi mai shekaru 33 wanda kuma yake sana'ar wanki da guga hukuncin daurin watanni 3.

Mun dai samu labarin cewa kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da ta gama tabbatar da cewa matashin ya saci tukunyar giyar gargajiya ta Burkutu inda kuma masu giyar suka maka shi kotun.

Kotu ta daure wani mai sana'ar wanki da guga watanni 3 saboda ya saci tukunyar burkutu
Kotu ta daure wani mai sana'ar wanki da guga watanni 3 saboda ya saci tukunyar burkutu

Legit.ng ta samu labarin cewa dai alkalin kotun mai suna Abubakar Sadiq ya kuma ba shi zabin biyan tarar N10,000 idan har baya son yayi zaman gidan yarin.

Haka ma dai kotun ta sake umurtar barawon da ya biya masu giyar kudin giyar tasu da ya sace kudin da suka kai N25,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel