Wata mai sayar da soyayya ta daba wa wani dan kasuwa kwalba har lahira, bayan ya saya yaki biyanta

Wata mai sayar da soyayya ta daba wa wani dan kasuwa kwalba har lahira, bayan ya saya yaki biyanta

- Wata mace mai siyar da soyaya ta halaka wani dan kasuwa a jihar Delta

- Matan ta daba masa wuka a ciki ne bayan yaki biyan kudin Karin lokaci

- Yanzu dai matar da ake tuhuma tana wajen yan sanda domin ci gaba da bincike

Wata mai sayar da soyaya ta soki wani dan kasuwa kwalba wanda yayi sanadiyar tafiyarsa lahira a wani sannanan hotel da ke kusa da Abraka Quarters a garin Asaba da ke jihar Delta bisa dalilin rashin biyan ta kudin sayar da soyayan.

Wata majiya ta tabbatar da faruwar lamarin a hotel din, hakan kuma ya haifar da tashin hankali saboda mazauna unguwar basu taba tsamanin mai siyar da soyayar zata aikata hakan ba.

Wata mai sayar da soyayya ta daba wa wani dan kasuwa wuka har lahira, bayan ya saya yaki biyanta
Wata mai sayar da soyayya ta daba wa wani dan kasuwa wuka har lahira, bayan ya saya yaki biyanta

Jami’an yan sanda da sukayi magana da jaridar Guardian amma sun nemi a sakaya sunansu sunce mai siyar da soyayar da tare dan kasuwan ne a lokacin da yake tsalakowa daga gadar Niger sannan ta daba mishi kwalba bisa dalilin rashin biyan ta da baiyi ba.

DUBA WANNAN: Sharhin The Economist, babbar jaridar Landan kan rashin lafiyar Buhari

Wanda abin ya faru a idon su sunce wadda ake zargi da kisan ta tare dan kasuwan ne wanda take zargin ya sha mugan kwayoyi wanda hakan ne yasa ya wuce lokacin da ta diba masa, hakan kuma bai yi mata dadi bai shi yasa ta nemi ya kara mata kudi. Bayan yaki ya kara mata kudin, sai ta fito da kwalba, ta fasa kwalbar sannan ta daba masa a ciki, tayi tafiyarta ta bar shi cikin jinni sannan daga bisani jami’an tsaro suka shigo hotel din.

Wani dan sanda da bai son a fadi sunnan sa da ke shelkwatan yan sanda na jihar ya tabbatar da cewa wadda ake zargi tana tsare domin yan sanda su cigaba da bincike.

A halin yanzu, jami’an tsaro sun rufe otel din, shi kuma Manaja da sauran ma’aikata sun tsere domin tsoron abin da zai biyo baya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng