Abubuwa 5 da su ka sa Marigayi tsohon Gwamnan Kano ya bar tarihi
Sabo Bakin-zuwo yayi Gwamnan Jihar Kano a shekarar 1983 bayan ya doke babban abokin hamayyar sa Abubakar Rimi. Kun dai ji cewa Sabo bai taba karatun Boko ba amma dalibi ne na Malam Aminu Kano.
1. An taba tambayar Sabo Bakin-Zuwo game da irin arzikin da ke Jihar Kano watau Minerals kawai sai ya fara Ambato Fanta, Mirinda, Coke, dsr
2. Sabo Bakin-Zuwo ya taba cewa ba ya zagin Jama’a amma fa duk wanda ya taba Aminu Kano sai ya ga waye Uban sa da Uwar sa
3. Gwamna Sabo Bakin-Zuwo ya taba cewa bai dace Direba yayi hadarin mota amma a kama karen-mota ba
4. Sabo ya taba yin kaca-kaca da Kanal Ahmadu Ali lokacin da aka nada sa Minista, yace shekaran Ali 10 a gidan Soji babu karin matsayi
5. A lokacin da aka kirkiro Jarrabawar JAMB, Marigayi Sabo yace ana kokarin a hana ‘Yan Arewa shiga Jami’a
Janar Buhari ya kifar da Gwamnatin kasar a Disambar shekarar 1983. Gwamnatin Sojar Buhari ta yankewa Sabo Bakin-zuwo da wani Kwamishinan sa shekaru 300 a gidan yarin Kiri-kiri.
Mun tsakuro wannan tarihi daga https://abiyamo.com
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Tsohon Shugaban kasa Jonathan a wani taro
Asali: Legit.ng