Majalisar dokoki ta jihar Kano ta jingine tantance mace a matsayin kantoma a jihar
Zaman majalisa ya dau zafi a jihar Kano bayan da Gwamnan Kano din ya tura sunayen yan jihar su 44 ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa a matsayin kantomomin riko a jihar.
Bayan zaman majalisar ne sai majalisar ta jingine matun tantance wata mace mai suna Hajiya Binta Yahaya tare da wasu mutanen har sai wani lokaci nan gaba bayan kura ta lafa.
Legit.ng ta samu labarin cewa majalisar dai ta amince da mutane 32 daga cikin 44 yayin da tayi watsi da mutane 3 saboda rashin cancantarsu, sai kuma guda 9 da ta jingine batun tantancesu sai an zurfafa bincike akansu.
Ita dai wannan mata wadda ke zaman daya tilo a cikin jerin mutanen da aka turawa majalisar tana da karatun digirin ta na biyu watau Masters a turance kuma malamar jami'ar kimiyya da fasaha ce ta jihar Kanon wadda ke a Wudil.
Asali: Legit.ng