Matata na mutsitsika mini ‘ya’yan marainai na Idan muna fada

Matata na mutsitsika mini ‘ya’yan marainai na Idan muna fada

Rahotanni sun kawo cewa wani magidanci mai suna Chukwuma dake jihar Lagas ya roki wata kotu da ta tsinke igiyar auren dake tsakaninsa da matarsa sakamakon yunkurin hallaka shi da take yi a kullun idan sabani ya shiga tsakaninsu.

A cewar sa a duk lokacin da abu ya hada shi da matar tasa sai ta kamo masa dan marainansa tayi ta murzawa wanda hakan kan gigitar da shi tare da sanya sa cikin wani mawuyacin hali.

Don haka ne yake rokon kotun da ta raba aurensa da matarsa wacce aka ambata da suna Obianuju.

Matar ta sa ta amince da abin da mijinta Chukwu ya nemi kotu tayi na raba aurensu domin ita ma a cewarta ta gaji da shan duka a hannunsa.

Matata na mutsitsika mini ‘ya’yan marainai na Idan muna fada
Matata na mutsitsika mini ‘ya’yan marainai na Idan muna fada

“Mijina yana mun dukan tsiya sannan yak an ji mini rauni. A kallun zaka samu cikina da tabon ciwo saboda dukan da yake mini.

“Ya taba cire mani hakori ta sanadiyar duka kuma ya kasance matsafi”.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP ba matsala ba ce - Okorocha

Obianuju ta ce ta taba kama mijinta na yi mata asiri cikin dare bai san ta tashi daga barci ba lokacin.

Alkalin Kotun dake sauraren karar ya daga ci gaba da haka zuwa watan gobe.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna son bamu shawara ko bamu labarai tuntube me a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel