Ilimi gishirin zaman Duniya: Yadda tsohuwa mai shekaru 74 ta samu kwalin digiri
- Wata tsohuwa ta samu shaidar digiri mafi daraja a Jami'a
- Ita dai wannan tsohuwa ta samu digiri ne tana shekaru 74
Wata dattijuwa bakar fata daga kasar Birtaniya ta kammala karatun digirin ta na farko tana da shekaru 74 a rayuwa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Jikar wannan mata mai suna Tasleigh Kay ce ta bayyana haka a shinta na Tuwita, inda tace ‘Kakata ta samu shaidar kammala karatun digirinta na farko tana shekaru 74, ina taya kaka murna.”
KU KARANTA: Toh fa! Za’a shirya Fim ɗin Shekau a Kannywood (HOTO)
Karin mamaki da wannan Dattijuwa da ba’a bayyana sunanta ba shine, ta kammala karatun nata ne da sakamako mafi daraja a fannin karatun fahimtar dan adam.
Sai dai dama dai ana yawan samun dattijai masu kokarin neman ilimi kuma har su samu shaidar kammala karatuttukansu musamman a nahiyar Turai, muma a nan Najeriya ba’a bar mu a baya ba, inda akwai tsarin koyarwa na yaki da jahilci ga manyan mutane da basu yi karatu a kuruciya ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Zaben Anambra, kalla:
Asali: Legit.ng