Jami'an tsaron farin kaya na Najeriya sun yi wa sauran jami'an tsaro kwakkwaran kashedi
Hukumar rundunar tsaron farin kaya watau DSS a takaice ta fitar da sanarwa tana mai yin kashedi ga sauran takwarorin ta na hukumomin tsaron Najeriya.
Hukumar ta DSS ta yi kashedin ne ga jami'an tsaron Najeriya da kuma hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa na kasar inda bukace su da su dena kwaikwayon ta wajen yin aikin su.
Legit.ng ta samu labarin cewa jami'in hulda da jama'a na hukumar Tony Opuiyo shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya sawa hannu ya kuma fitar tare da rabawa ga manema labarai.
Mista Tony har ila yau a cikin takardar ya bayar da misali da yadda wasu jami'an tsaron suka kai samame a gidan tsohon jami'in gwamnati Namadi Sambo da cewa sune kawai ke da hurumin yin irin wannan samamen.
Sanarwar ta kuma ce ba ita ta kai samamen da aka kai wani ofishin kamfanin makamashi na Sahara Energy Company a Abuja ba.
Asali: Legit.ng