Adam Zango yace an taba hana shi aure don ana zargin yana luwadi

Adam Zango yace an taba hana shi aure don ana zargin yana luwadi

- A cikin jaruman kasar Hausa na Kannywood, Adam Zango yayi fice

- Ya kare kansa kan batun zargin luwadi

- Yace har aure aka hana shi kan wannan zargi a baya

A kasar Hausa dai, akwai wasu dabi'u da koda a wasu kasashen ba abun ki bane, suna iya jaza wa mutum jafa'i, cikin su kuwa harda zargin luwadi, neman maza dai a gwamnatance da shariar addini da ma al'ada, duk abun ki ne a fili.

Adam Zango yace an taba hana shi aure don ana zargin yana luwadi
Adam Zango yace an taba hana shi aure don ana zargin yana luwadi

A kimiyyance dai, masana sun ce auratayya ta jinsi bata da illa, ko ta madigo, ko ta luwadi, musamman zaman cewa a halittar wasu, akwai mata-maza, dama fahimtar menene sinadarin Oestrogen da Testosterone wanda ke cikin jini, wanda shi yake gaya wa kwakwalwa ita namiji ce ko mace, da ma cewa wa zata nema a matsayin abokin saduwa. Haka kuma a da ba'a tsangwamar 'yan daudu, sai da aka fara shari'ar Islama a 'yan shekarun nan.

A tsakanin al'umma ma dai, da anga wani ya faso gari, ko yayi kudi farat daya, sai a fara masa zargi ko na sata, ko tsafi, ko neman maza, ko ma hulda da wai aljannu. A haka sai a yi ta yi wa mutum sharri a kuma kyamace shi.

DUBA WANNAN: Zargin jihadi ga al'ummun Arewa, an mayar wa da masu zargi martani

Hakan ta kai jarumi Adam Zango, da har sai da ya kai ga rantsuwa da Kur'ani, a lokuta da dama domin ya cire wa kansa wannan zargi, da jama'a ke yamadidi da shi, wanda a cewarsa, har aure aka taba hana shi bisa hakan.

'Yan siyasa ma dai, da hamshakan malamai, ana musu irin wannan zargin, inda yakan zama kashin kaji da ake shafa musu don jama'a su kyamace su, wanda babu komai ciki sai bukulu da sharri.

Allah shi kyauta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng