Shekaru Uku kenan da na raba jaha da Nafisa Abdullahi a soyayya – A Zango

Shekaru Uku kenan da na raba jaha da Nafisa Abdullahi a soyayya – A Zango

- Adam A Zango ya tabbatar da soyayyarsa da Nafisa Abdullahi

- Sai dai yace sun rabu kimanin shekaru 3 da suka gabata

Shahararren dan wasan Hausa Fim, Adam a Zango ya bayyana cewar gaskiya ne ya taba yin soyayya da fitacciyar jarumar Kannywood, Nafisa Abdullahi, a wata hira da yayi da BBC Hausa.

A zango ya bayyana ma majiyar Legit.ng ya taba soyayya da Nafisa, amma zuwa yanzu, kimanin shekaru 3 kenan basa tare.

KU KARANTA:

“Gaskiya ne, nayi soyayya da Nafisa, Amma yanzu kimanin shekaru uku kenan bama tare.” Inji Adam Zango.

Shekaru Uku kenan da na raba jaha da Nafisa Abdullahi a soyayya – A Zango
Nafisa Abdullahi da A Zango

A baya ma an sha yayata labarin cewar dantaka tayi tsami tsakanin Adam Zango da Nafisa, inda hakan ya kaisu ga shiga kotu, sai dai daga bisani, manya sun shiga maganar, inda daga karshe aka yi musu sulhu.

A wani labarin kuma, A Zango yace babban burinsa a rayuwa shine yak ware wajen magana da yaren Turanci, don haka ne ma yace yana da sha’awar komawa makaranta, don samun koda difloma ce.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Shin ya dace a dade ana soyayya kafin aure? Kalla:

Asali: Legit.ng

Online view pixel