Matasan APC sunyi kira ga kamun Psquare (hoto)

Matasan APC sunyi kira ga kamun Psquare (hoto)

- Kwanan nan gwamnatin tarayya ta sanar da cewa an dakatar da dukkan mawaka daga yin wakokinsu a kasashen waje

- Dakatarwan da gwamnatin tayi ya hanyo martani daga Peter Okoye daya daga cikin kungiyar P-square

- Peter Okoye ya zagi gwamnatin tarayya a shafin zumunta bayan an sanar da dakatarwan

Sakamakon harin da Peter Okoye ya kai ga gwamnatin Najeriya, wata kungiyar matasa mai suna Youth Renaissance, da tayi ikirarin kasancewa daga cikin jam’iyyar APC, ta yi kira ga kamun P-square.

Legit.ng ta rahoto cewa dan uwan P-square, Peter Okoye, ya bayyana cewa yana kunyar kasar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta gaza tun shekarar 1960.

Yayinda suke maida martani ga furucin Peter, kungiyar ta bukaci hukumomin tsaro da su kama shi kan furucin matanci da ya yi game da gwamnatin.

Matasan APC sunyi kira ga kamun Psquare (hoto)
Matasan APC sunyi kira ga kamun Psquare Hoto: Instagram Peter Okoye

Collins Edwin, sakataren kungiyar, ya bayyana cewa hukuncin gwamnati na dakatar da shirya wakoki a waje tayi hakan ne domin ta samar da aiki a hukumomin nishadantarwa.

KU KARANTA KUMA: Ta biya 10,000 a kashe mijinta saboda ya yi mata kishiyaTa biya 10,000 a kashe mijinta saboda ya yi mata kishiya

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng