‘Yan Najeriya sun nemi a fito da hoton Shugaba Buhari

‘Yan Najeriya sun nemi a fito da hoton Shugaba Buhari

- Tun tafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari har yau ba a ga hoton sa ba

- Ko da dai ya aikowa mutanen Kasar sakon karamar Sallah da harshen Hausa

- Ana ta yada wasu tsofaffin Hotuna a matsayin hotunan Shugaban kasar na kwanan nan

Ku na sane cewa tun bayan tafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari har yau ba a ga hoton sa ba illa dai wani sakon da ya aiko lokacin bikin karamar Sallah ga Musulman kasar.

‘Yan Najeriya sun nemi a fito da hoton Shugaba Buhari
Hoton Osinbajo lokacin da ya gana da Shugaba Buhari

Ko da dai Matar shugaban Hajiya Aisha Buhari da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo sun samu ganawa da shi a Birnin Landan kwanaki amma har yau babu wanda ya ga hoton ganawar ta su inda Jama'a su ka fara kokawa.

KU KARANTA: Wani Bawan Allah yace Zahra ta gaida Buhari

‘Yan Najeriya sun nemi a fito da hoton Shugaba Buhari
Har yanzu an rasa gani hoton Shugaba Buhari

Daya daga cikin masu ba Shugaban kasar shawara Malam Bashir Ahmad yace kusan duk hotunan Shugaba Buhari da ake yadawa tsofaffi ne ba kwanan nan aka dauka ba inda yake maidawa wani Malam Ashaka Saleh martani bayan ya dauko wani tsohon hoto yana yadawa.

Mun dai bi diddigi dsga Jaridu irin mun gano wasu daga cikin wadanda su ka iya ganawa da Shugaba Buhari tun bayan fitar sa Landan. Daga ciki akwai wasu Ministoci 2.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya sun fara neman Shugaban Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel