Wani Bawan Allah ya fadawa Zahra Buhari ta gaida Baban ta
- Zahra Buhari tayi alkawarin aika sakon Wani Dan Najeriya wajen Shugaba Buhari
- Wani Bawan Allah ya nemi Diyar Shugaban kasar Zahra ta gaida Baban ta
- Ita kuwa tace In Allah ya so ya yarda kamar a kunnen sa da zarar sun yi waya
'Yar lelen Shugaban Kasa watau Zahra Buhari tayi alkawarin aika sakon gaisuwar da addu'ar wani Dan Najeriya mai suna Aminu da zarar da tayi waya da Shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda yake jinya.
Malam Muhammad Ameenu ya fadawa Zahra Buhari hakan ne a shafin sa na Tuwita inda yake cewa don Allah a duk lokacin da tayi waya da Baba Buhari ta fada masa cewa yana masa addua ta samun lafiya.
KU KARANTA: Saraki ya gagara ganin Shugaba Buhari a Landan
Zahra Buhari wanda tayi aure a karshen bara ga Ahmed Muammmad Indimi tace idan Allah ya yarda kuwa za ga fadawa Baban na ta. Wannan Bawan Allaah dai yayi wa Najeriya gaba daya addua a sakon na sa.
Shi kuma Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose ya kara jaddada cewa shi zai karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Fayose yace yanzu ya fara kokarin tattaro jama'a da za su mara masa baya
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ana magana game da Ministocin Buhari
Asali: Legit.ng