Gwamnatin tarayya ta daidaita albashin masu digiri da babban diploma
-Gwamnatin tarayya ta amince da biyan albashi iri daya ga masu digiri da babban diploma
-Babbanci tsakanin albashin masu digiri da babbar diploma ta kau
Mutane sun dade suna neman gwamnatin tarayya ta kawo karshen banbancin albashi tsakanin ma’aikata masu digiri da kuma masu babbar diploma (HND)
Gwamnatin tarayya ta amsa wannan kira domin ta kawo karshen babbancin da ke tsakanin ma’aikata masu takardan karatu na digiri da kuma masu babban diploma a wasu hukumomin tarayya.
Domin tabattar da canjin, gwamnatin tarayyan ta bada umarnin Karin girma ga masu babban diplomar zuwa mataki na 8 wanda shine matakin da masu digiri suke. Hukumomin da aka ba wannan umarnin sun hada da hukumar shige da fice wato (kwastam), hukumar kare gobara, hukumar kulla da gidajen yari da kuma civil defence.
KU DUBA: Zargin rashin jituwa tsakanin Osinbajo da Buhari da Ministoci, Lai Muhammed yayi karin haske
A wata sanarwa da ta fito ta bakin sakataren ma’aikatan harkokin cikin gida, Abubakar magaji yace ministan harkokin cikin gidan Lt. Gen. Abdulrahman Dambazau a ya hannu a takarda domin amincewa da daidaita albashin a wata taro da sukayi ranar Talata a garin Abuja.
Sanarwan tace, “Mahukuntan ma’aikatan sun bada umarnin daga darajar ma’aikata masu babbar diploma zuwa mataki na 8, wanda shine matakin farko da ake daukan masu digiri a farkon aiki.
“Koda yake za’a kira masu babban diploma da mukamin babban sipeta, za’a kira masu digiri da mukamin mataimakin supritenda na 2.”
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng