Wasan kwaikwayo: Wacece Fati Washa?

Wasan kwaikwayo: Wacece Fati Washa?

- Yau dai mu na jin lekawa ne zuwa Filin wasan kwaikwayon Hausa

- Mun kara kawo maku tarihin wata babbar ‘Yar wasan fim din Hausa

- Wannan ba kowa bace sai jarumar nan ta wasan kwaikwayo Washa

Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta san ta.

Wasan kwaikwayo: Wacece Fati Washa?
Hoton 'Yar wasa Fati Washa daga wani fim

Jama’a sun fi sanin ta da Washa ko kace Tara washa ko ma Fati Washa watau sunan Mahaifin ta ya bace. Kadan daga cikin fina-finan wannan Jaruma akwai Ya Allah da tayi a 2014, 'Yar Tasha a 2015 Washa ta fito a Ana Wata ga Wata a shekarar 2015.

KU KARANTA: Kemi Adeosun ta gargadi Najeriya

Wasan kwaikwayo: Wacece Fati Washa?
Jarumar 'Yar Wasan kwaikwayo Washa

Fati Washa kamar su Rahma Sadau, Hadiza Gabon, da 'Dan wasa Ali Nuhu, dsr tana kan shafin Tuwita na yanar gizo inda ta ke aikawa dinbin masoya da mabiyan ta sako da game da halin rayuwa da harkar soyayya.

Dazu kun ji tarihin Halima Atete, wand aba batun ba fim kadai ba, ta yi karatun Boko a Garin Maiganari daga nan kuma ta koma wata Makaranta a Garin Yerwa. Daga baya ma ta koma Kwalejin nan ta Mohammed Goni inda tayi difiloma a shari’a.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ruwa yayi gyara a wurare da dama a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng