Mai mata 12 da 'ya 'ya 100 yace bai gaji da haihuwa ba

Mai mata 12 da 'ya 'ya 100 yace bai gaji da haihuwa ba

- Wani mutumi 'Dan kasar Ghana ya haifi 'ya 'ya fiye da 100

- Amma fa yace so samu ya kara samun wasu ‘ya ‘yan

- Wannan ta’aliki yana da mata har 12 a halin yanzu

Gidan BBC tayi hira da wani mutumi 'Dan kasar Ghana da ya haifi 'ya 'ya fiye da 100 a Duniya kuma yace har yanzu bai gaji da samun yaran ba.

Mai mata sha biyu: Wani mai 'ya 'ya 100 yace bai gaji da haihuwa ba
Hoton Kofi Asilenu Mai mata sha biyu daga BBC

Kwanan nan aka yi bikin al'umma ta Duniya inda wannan mutumi mai suna Kofi Asilenu a wani Kauye cikin Kasar Ghana mai 'ya 'ya 100 da mata 12 yace shi fa har gobe in zai samu karin 'ya 'ya yana so.

KU KARANTA : Dubi inda Dalibai ke karatu a Zamfara

Wannan mutumi yace bai da kowa a Duniya na Danuwa don haka ya dage wajen tara 'diya. Asilenu yace duk da shekarun sa 80 amma har yanzu da karfin sa don haka so ma yake ‘ya ‘yan na sa su wuce haka.

Abin da ba a taba gani ko ji a Kasar Ingila ba ya faru don kuwa wasu Musulmai maza ne su ka auri junan su hankali kwance a wata Unguwa kwanan nan.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda Gwamnan Jihar Osun ya ciri tuta

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel