Lafiya uwar jiki! Anfanin ganyen Lansur 7 a jikin dan adam

Lafiya uwar jiki! Anfanin ganyen Lansur 7 a jikin dan adam

- Lafiya Uwar jiki ce

- Alfanun ganyen Lansur 7 a jikin dan adam

A ci gaba da muke yi wajen kawo maku labaran da ke da alaka da lafiyar jikin ku yau kuma zamu kawo maku anfani 7 da ganyen na na Lansur keyi a jikin dan adam.

Legit.ng dai ta samu cewa akan sarrafa ganyen na Lansur ta hanyoyi da dama kamar dai sauran ganyayyaki domin ci ko kuma sawa a abinci.

Ga dai wasu daga cikin anfanonin sa:

1. Bincike ya nuna cewa ganyen Lansur yana da matukar tasiri wajen kara karfin gani da kuma lafiyar ido.

2. Haka ma an bayyana cewa yana maganin muguwar cutar nan ta hawan jini.

3. Haka ma dai an bayyana cewa yana da matukar tasiri wajen magance cututtukan fata kamar su kyasfi da dai sauransu.

Lafiya uwar jiki! Anfanin ganyen Lansur 7 a jikin dan adam
Lafiya uwar jiki! Anfanin ganyen Lansur 7 a jikin dan adam

4. Bikici kuma ya tabbatar da cewa Lansur din yakan daidaita wa mutum yanayin cin abincin sa.

5. Haka ma dai an bayyana ganyen a matsayin abincin dake maganin ciwon ciki da bacin sa.

6. Kamar dai yadda bincike ya nuna, ganyen na Lansur yana maganin ciwon zuciya.

7. Ance kuma Lansur din yana maganin kwarnafi, tashin zuciya da kuma amai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng