Iyaye su dage wajen sanya ýaýansu haddar Al-Qur’ani domin gyaran al'umma – Sarkin Musulmi
- Sarkin Musulmi ya koka kan yadda yawaitan amfani da kafafen sadarwa ke shafar karatun yan mata
- Sarkin ya karrama wata daliba mahaddaciya data lashe gasan Al-Qur'ani
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya nayyana damuwarsa dangane da yadda kafafen sadarwa na zamani ke kawar da hankulan daliba a kasar nan.
Sarkin ya nuna wannan damuwa tasa ne a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli yayi rufe gasan Al-Qur’ani na kasa daya gudana a jihar Sakkwato, inda yace: “Abin damuwa ne yadda shafukan sadarwa ke dauke hankulan yayan mu daga karatuttukansu.
KU KARANTA: Sama da mamena aiki 500 ne za’a tantance a jihar Kaduna – KARANTA
“Kafafen sadarwa irin su Facebook, Whatsapp, Twitter, 2go da Intagram na duake hankulan yayan mu. Matalsar tafi shafan yan matan mu, musamman yadda sune iyayen al’umma, idan suka gurau kowa ya gyaru.” Inji Sarkin.
Kamfanin dillancin labaru ta ruwaito, Sarkin yana shawartar iyaye dasu dage wajen ganin yayansu sun yi haddara Qur’ani, tare han kunnen musulmai da su guji duk wani hali da ka iya baya sunan addinin su.
A karshen taron, wanda tazo ta daya a gasar, Husna Nura daga jihar Katsina ta kyautar N100,000 daga wajen Sarkin Muslmi Sa’ad, sa’annan shima gwamnan jihar ya bata kyautan N150,000, kujeran Makkah da na’aurar samar da kankara.
Yayin da sauran mahaddatan da suka fafata a gasar suka samu kyautan N10,000 duk mutum daya daga Sarkin, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wai ina Buhari ya shiga ne?
Asali: Legit.ng